27 Yuni 2021 - 13:59
Gwamnan Borno Ya Dakatar Da Wata Кungiyar Agaji Ta Faransa Saboda Koyawa Mutane Harbi

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da umarnin dakatar da wata ƙungiyar agaji mai zaman kanta ta ƙasar Faransa (ACTED) saboda tana bayar da horon harbin bindiga a wani otal a birnin Maiduguri, babban birnin jihar.

ABNA24 : Yayin da ya ke sanar da hakan ga manema labarai a jiya Asabar, kakakin gwamnan Isa Gusau ya ce jami’an ‘yan sanda da suka je wajen bayan labarin sirri da suka samu sun samu kananan bindigogi da sauran nau’oin makamai irin wannan a babban ɗakin da ake ba da horon harbin.

Kakakin ya ci gaba da cewa don haka gwamnatin jihar Bornon Babagana Umara Zulum ya ba da umurnin dakatar da ayyukan ƙungiyar ta ACTED sakamakon wannan aikin da take yi.

Sanarwar dai ta ci gaba da cewa ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda suna tsare da wasu mutane biyu da aka kama a wajen suna ba da horon, sannan kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

An jima dai ana zargin wasu ƙungiyoyin ba da agaji musamman waɗanda suka zo daga ƙasashen waje da hannu cikin ayyukan ta’addanci da kuma taimaka wa ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da suke gudanar da ayyukansu a jihar Bornon.

342/